Hukumar 'Yan sanda ta tanadi Jami'ai 5000 da Makamai domin Gangamin APC a Garin Abuja

Hukumar 'Yan sanda ta tanadi Jami'ai 5000 da Makamai domin Gangamin APC a Garin Abuja

Hukumar 'Yan sanda ta Najeriya ta yi tanadin jami'ai 5000 domin gangamin jam'iyyar APC da aka shirya gudanarwa a gobe da yayi daidai da ranar 23 ga watan Yuni a babban birnin kasar nan na Abuja kamar yadda shafin jaridar PM News ya bayyana.

Kakakin hukumar 'yan sanda na kasa DCP Jimoh Moshood, shine ya bayar da wannan sanarwa a ranar Juma'ar da ta gabata inda ya bayyana cewa, Sufeto Janar na 'yan sanda Mista Ibrahim K. Idris, shine ya bayar da umarnin aiwatar da wannan shiri domin tabbatar da matsanancin tsaro yayin gudanar da gangamin na jam'iyyar APC a garin Abuja.

Yace an sanya 'yan sandan sama da kuma rundunar jami'an masu rike da makamai a ƙarƙashin kulawar Mataimakin Sufeto Janar na 'Yan sanda, domin tabbatar da tsaro mai inganci ga mahalarta taron.

Hukumar 'Yan sanda ta tanadi Jami'ai 5000 da Makamai domin Gangamin APC

Hukumar 'Yan sanda ta tanadi Jami'ai 5000 da Makamai domin Gangamin APC

DCP Moshood yake cewa, an tanadi jiragen sama masu saukar ungulu guda biyu da kuma manyan motocin yaki guda shida masu dauke da makamai domin tabbatar da tsaro a taron.

KARANTA KUMA: Mu na goyon bayan sauya Fasalin 'Kasa - Osinbajo

Legit.ng ta fahimci cewa, hukumar 'yan sanda ta kuma tanadi jami'ai na wasu hukumomin tsaro na daban tare da gargadin su kan sanya kakakin hukumar su domin dafawa jami'an 'yan sanda wajen tabbatar da tsaro yayin gudanar da taron.

Kakakin hukumar ya ci gaba da cewa, wakilan jami'iyyar masu takardu na shaidar tantancewa ke da dama ta shiga farfajiyar wannan taro yayin da ya gargadi duk wadanda ba su da hurumi a taron akan kada su kuskura su kusanci farfajiyar taron.

Kazalika kakakin ya nemi daukacin al'umma masu korafi ko wane hangen nesa dangane da harkar tsaro akan su kiraya wadannan lambobi; 08032003913, 08061581938 da 07057337653 domin shigar da rahoton su cikin gaggawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel