Kocin Iceland ya bayyana dalilin da ya sa suka sha kashi a hannun Super Eagles ta Najeriya

Kocin Iceland ya bayyana dalilin da ya sa suka sha kashi a hannun Super Eagles ta Najeriya

- Kocin kasar Iceland ya bayyana cewa kadara ce ta sa suka sha kaye a hannun Najeriya

- Kocin ya ce shi da 'yan wasan sa sunyi dukkan shirin da ya kamata suyi kafin buga wasan

- Duk da haka, kocin ya yabawa kokarin da yan wasarsa na kasar Iceland din su kayi

Heimir Hallgrimsson, mai horas da yan wasan kwallon kafa na Iceland ya ce kadara ce ta sa Super Eagles ta Najeriya tayi nasara a kan kasar Iceland a wasan da suka tashi da ci biyu da nema a gasar cin kofin duniya na kwallon kafa ne shekarar 2018 da ake bugawa a Rasha.

Kocin ya ce yan wasansa sunyi biyaya ga dukkan dokokin da ya gindaya musu, kuma kawai don ba suyi nasara ba baya nufin basu tabuka komai ba.

Kocin Iceland ya bayyana dalilin da ya suka sha kashin a hannun Super Eagles

Kocin Iceland ya bayyana dalilin da ya suka sha kashin a hannun Super Eagles

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya taya Super Eagles murnar samun nasarar wasan yau

"Ina alfahari da yan wasan nawa saboda sun buga wasa da kungiya mai karfi kamar ta Najeriya" kamar yadda ya fadi a filin Volgograd bayan kammala wasan a yau.

Sai dai duk da hakan kocin ya amsa cewa dabarun da kungiyarsa su kayi amfani dasu ba suyi tasiri kamar yadda su kayi tsamanin za tayi ba.

"Bamu ji dadin yadda muka sha kashi a wajen Najeriya ba duk da irin shirin da mu kayi kafin wasan

"Munyi iya kokarin mu wajen shirye-shirye, musamman yadda muka saka masu tsaron gida guda uku. Har ma munyi shirin amfani da masu tsaron gida hudu," inji shi.

A wata labarin, Legit.ng ta kawo muku cewa shugaba Muhammadu Buhari ya mika sakon murnarsa ga yan wasan ta Super Eagles bisa nasarar da suka samu a yau.

Shugaban kasan kuma ya bukaci su kara himma da kaimi musamman a wasan su ta gaba inda za su kara da Argentina a mako mai zuwa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel