Buhari yayi sabbin nadi masu muhimmanci a hukumomin tarayya

Buhari yayi sabbin nadi masu muhimmanci a hukumomin tarayya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin sabbin shugabanni a hukumomin tarayya sannan kuma ya sabonta wasu.

Labarin nade-naden na cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Olusegun Adekunle, sakataren din-din-din na ofishin babban sakataren gwamnatin tarayya a ranar Juma’a a Abuja.

An zabi Mista Adeola Adetunji, Farfesa Mike Obadan, Farfesa Justitia Nnabuko da kuma Farfesa Ummu Jalingo a matsayin daraktoci a babban bankin kasar CBN.

Bisa ga sanarwan, nadin zai fara aiki daga ranar 7 ga watan Yuni, 2018 na tsawon shekaru hudu.

KU KARANTA KUMA: Mambobin APC da PDP 10,000 sun sauya sheka zuwa jam’iyyar Obasanjo

Sannan an nada Farfesa Abdullahi Dasilva Yusuf a matsayin babban daraktan lafiya, asibitin koyarwa na Ilorin, na tsawon shekaru hudu wanda zai fara daga ranar 19 ga watan Yuni 2018.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel