An gano dansandan dake da biliyan biyu a makare a bankinsa

An gano dansandan dake da biliyan biyu a makare a bankinsa

- Majiyar mu ta ruwaito cewa sunan shi sifeto Christopher Marcel Nnabugwu, wanda ke aiki a bangaren binciken ta'addanci na reshen yan sandan Ogudu a Legas

- An gano yadda wata budurwar da bata bayyana fuskar ta ba a wani video, ta fadi sunan Dan sandan tare da kira ga sifeto Janar na yan sanda da ya binciki silar arzikin Dan sandan

An gano dansandan dake da biliyan biyu a makare a bankinsa

An gano dansandan dake da biliyan biyu a makare a bankinsa

Kwamishinan yan sandan jihar Legas, Imohimi Edgal, ya bayyana sunan Dan sandan da ake zargi da mallakar Naira biliyan 2 a asusun bankin shi.

Majiyar mu ta ruwaito cewa sunan shi sifeto Christopher Marcel Nnabugwu, wanda ke aiki a bangaren binciken ta'addanci na reshen yan sandan Ogudu a Legas.

Legit.ng ta gano yadda wata budurwar da bata bayyana fuskar ta ba a wani video, ta fadi sunan Dan sandan tare da kira ga sifeto Janar na yan sanda da ya binciki silar arzikin Dan sandan.

An ruwaito cewa budurwar tace Nnabugwu yana da kadara ta gida a lamba 27,Fani Kayode Street, dake GRA, Ikeja wanda zai yi kimanin Naira miliyan 250.

Ta kuma zargi Dan sandan da amfani da motar alfarma mai lamba da tambarin 'MCON' kuma duk lokacin da ya shiga kulop din dare, sai kaji ana ihu da rige rigen biya mishi bukatun shi.

Ta kara da zargin cewa sajan din yana da kimanin Naira biliyan 2 kuma ya kashe miliyoyi a bikin murnar cikar shi shekaru 30 wanda akayi watan da ya gabata a wata kulop dake tsibiri.

DUBA WANNAN: Najeriya ta doke Iceland

Sifeto Janar din yan sanda yayi Kiran gaggawa ga kwamishinan yan sandan jihar Legas don fara bincike.

Kwamishinan da kanshi ya jagoranci binciken inda ya gano cewa gidan ba na Nnabugwu bane.

Imohimi yace Christopher Nnabugwu da aka binciko dai bashi da wata motar alfarma, a gidan haya yake kuma asusun bankin shi guda biyu an duba Naira 15,000 ne a daya, dayan kuma Naira 5000.

Ana nan ana kokarin gano budurwar domin tayi kokarin bata wa yan sanda suna.

A halin yanzu dai hukumar yan sandan na neman ta ruwa a jallo.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel