Ko ta yaya Shaihun Malami ya kare da laifin hukuncin kisa?

Ko ta yaya Shaihun Malami ya kare da laifin hukuncin kisa?

- Wani Dan kunar bakin wake ya kai harin gurin shan shayi na Starbucks

- Malamin shine shugaban wata kungiyar masu tsattsauran ra'ayin addinin Islama dake kasar

- An daure Aburrahman a gidan Yari ne tun shekarar 2010,inda aka gano yana shirya hare hare duk da yana garkame

Ko ta yaya Shaihun Malami ya kare da laifin hukuncin kisa?

Ko ta yaya Shaihun Malami ya kare da laifin hukuncin kisa?

An yanke wa malamin addinin musulunci mai suna Aman Aburrahman hukuncin kisa, sakamakon kama shi da laifin shirya harin da yan ta'adda suka kai a 2016 birnin Jakarta wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane 4.

Wani Dan kunar bakin wake ya kai harin gurin shan shayi na Starbucks.

Malamin shine shugaban wata kungiyar masu tsattsauran ra'ayin addinin Islama dake kasar.

An daure Aburrahman a gidan Yari ne tun shekarar 2010, inda aka gano yana shirya hare hare duk da yana garkame.

A harin da aka kai Starbucks, ya hada da ofishin jami'an tsaro. Inda daga baya kuma yan bindiga dadi suka far wa mashaya shayin da harbi. Amma sunyi musayar wuta da yan sanda suka iso.

DUBA WANNAN: Najeriya 2-0 Iceland

An kashe mahara biyu, inda biyu kuma suka tada bam din da ke jikin su.

A ranar juma'a ne alkali ya yankewa Aburrahman hukuncin sakamakon laifin da aka kama shi dashi na "aiwatar da ta'addanci"

Aburrahman ya musa hakan kuma yace ya umarci magoya bayanshi dasu je Syria su yaki IS ne, ba wai su kai hari Indonesiya ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel