Yanzu Yanzu: Jami’an DSS sun mamaye gidan Sanata Abaribe na Abuja

Yanzu Yanzu: Jami’an DSS sun mamaye gidan Sanata Abaribe na Abuja

Jami’an hukumar yan sandan farin kaya DSS sun mamaye gidan Sanata Enyinnaya Abaribe na Abuja.

Majiyoyi sun bayyana cewa jami’an sun mamaye gidan wanda ke ayin gidan yan majaisa na Apo da misalin karfe 5:30 na yammacin ranar Juma’a da taimakon Abaribe.

A lokacin kawo wannan rahoton, an hana mutane shiga ko fita daga gidan. An tattaro cewa jami’an sun kuma binciki gidan inda daga bisani suka koma ofishin su da Abaribe.

Yanzu Yanzu: Jami’an DSS sun mamaye gidan Sanata Abaribe na Abuja

Yanzu Yanzu: Jami’an DSS sun mamaye gidan Sanata Abaribe na Abuja

KU KARANTA KUMA: Kasafin kudin Buhari, ba na kasa baki daya ba ne, na kasar Yarbawa ne - Shugaban Kungiyar cigaban matasan Arewa

A farkon ranar yau ne dai hukumar ta DSS ta kama sanatan a wani otel inda ta tisa keyarsa zuwa ofishin ta.

A baya Legit.ng ta tattaro cewa Mambobin PDP da na APC sama da guda 10,000 sun sauya sheka daga jam’iyyun su zuwa jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a ranar Alhamis, 21 ga watan Yuni.

Vanguard ta ruwaito cewa masu sauya shekar sun kasance mabiyan Sanata Olamilekan Adeola wanda aka fi sani da Yayi, dake wakiltan yankin Lagas na Yamma ne.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel