Mutane 6 sun yiwa wata Yarinya Fyade har Lahira a Jihar Anambra

Mutane 6 sun yiwa wata Yarinya Fyade har Lahira a Jihar Anambra

A wani kauyen Ogwugwu dake karamar hukumar Idemili ta Kudu a jihar Anambra, wasu Mutane shida suka yi tarayya da juna wajen yiwa wata yarinya fyade da shekarunta ba su wuci 17 a Duniya ba.

Marigayiyar da ba ta dade da kammala jarrabawar kare sakandire ba, ta gamu da wannan azal ne yayin da ta fito sayen garin kwakwi na yin karin dare inda mazajen shida suka far ma ta har lahira da misalin karfe 7.00 na yammacin ranar Larabar da ta gabata.

Mutane 6 sun yiwa wata Yarinya Fyade har Lahira a Jihar Anambra

Mutane 6 sun yiwa wata Yarinya Fyade har Lahira a Jihar Anambra

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya bayyana, wannan miyagu sun yadari yarinyar ne zuwa wani kango inda suka yi ma ta fyade daya bayan daya har lahira.

KARANTA KUMA: Ba mu da tanadin Fulotai domin kafa Yankunan Kiwon Shanu - Jihar Ebonyi ga Gwamnatin Tarayya

Legit.ng ta fahimci cewa, a halin yanzu tuni an mika gawar wannan yarinya zuwa dakin killace gawarwaki dake wani asibiti a yankin na Idemili.

Shugaban ofishin 'yan sanda na reshen Ojoto, Prince Ezejiofor, ya tabbatar da afkuwar wannan mummunan lamari sai dai ya bayyana cewa kawowa yanzu ba bu ko mutum guda da ya shiga hannu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel