Mambobin APC da PDP 10,000 sun sauya sheka zuwa jam’iyyar Obasanjo

Mambobin APC da PDP 10,000 sun sauya sheka zuwa jam’iyyar Obasanjo

Mambobin PDP da na APC sama da guda 10,000 sun sauya sheka daga jam’iyyun su zuwa jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a ranar Alhamis, 21 ga watan Yuni.

Vanguard ta ruwaito cewa masu sauya shekar sun kasance mabiyan Sanata Olamilekan Adeola wanda aka fi sani da Yayi, dake wakiltan yankin Lagas na Yamma ne.

Masu sauya shekar wanda aka fi sani da Yayi Movement sunce sun gaji da kungiyar sannan kuma cewa a shirye suke su koma ADC domin goyon bayan dan takarar gwamna Gboyega Isiaka a zaben 2019.

Mambobin APC da PDP 10,000 sun sauya sheka zuwa jam’iyyar Obasanjo

Mambobin APC da PDP 10,000 sun sauya sheka zuwa jam’iyyar Obasanjo

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa jam’iyyar ADC ta yi barazanar tada zaune tsaye a fadar shugaban kasa idan gwamnati mai ci ta taba Olusegun Obasanjo, tsohon shugaban kasar Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Labari mai dadi: Jiragen ruwa 34 cike da man fetur, abinci da sauran kayayyakin amfani na shirin isowa Lagas

Jam’iyyar wacce ta kasance ta Obasanjo ta yi wannan furci ne a kokarinta na maida martini ga ikirarin tsohon shugaban kasar na cewa gwamnatin Buhari na shirya makirci domin tsare shi akan hujjojin karya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel