Yanzunnan Najeriya ta lallasa Iceland da ci biyu ba ko daya, dan da kyar!

Yanzunnan Najeriya ta lallasa Iceland da ci biyu ba ko daya, dan da kyar!

- Wasan Najeriya yayi armashi!

- An tsorata Najeriya zata dawo gida da wuri

- Ahmad Musa ne ya ci duk kwallayen

Yanzunnan Najeriya ta lallasa Iceland da ci biyu ba ko daya, dan da kyar!

Yanzunnan Najeriya ta lallasa Iceland da ci biyu ba ko daya, dan da kyar!

Wasan da aka gama yanzunnan tsakanin Najeriya da Iceland, an tashi ci biyu da nema, inda Ahmed Musa ya zura dukkan kwallayen a raga bayan wasa mai kyau da hadin kai da Super Eagles din suka taka.

An dai dade ba'a ga irin wannan wasa ba a shafin tarihin kwallon Najeriya, watakil tun zuwansu wasan na farko a 1994, wanda marigayi Rashidi Yekini ya jefa kwallon farko.

A wasan kashi na farko dai, kamar Najeriya baza ta taka wani abin kirki ba, sai dai a karo na biyu, kamar an musu allurar kishin kasa, domin sun san in suka dawo gida a haka zasu ji kunyar idon jama'a sosai.

DUBA WANNAN: Labaran Hausa da dumi-duminsu

Garuruwa da Unguwanni dai sun dauki sowwa a duk lokutan da yaro maii tashe Ahmed Musa ya zura kwalayen, bayan sun wahal da turawan na Iceland.

A ranar talata Najeriya zata buga da uwar kwallo Argentina.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel