Zaben fid da gwani na PDP: Ko nayi nasara ko kada nayi nasara ina tare da PDP – Atiku Abubakar

Zaben fid da gwani na PDP: Ko nayi nasara ko kada nayi nasara ina tare da PDP – Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma babban jigo a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya sha alwashin yin aiki domin cigaban jam’iyyar, imma yayi nasarar samun tikitin tsayawa takarar shugabancin kasa ko akasin haka.

Dan takarar shugabancin kasa na 2019 din ya bayyana hakan ne a jiha a Wadata Plaza, babban sakatariyar PDP na kasa dake Abuja.

Atiku wadda ya ziyarci hedkwatar jam’iyyar domin sanar da kwamitin aiki na jam’iyyar (NWC) kudirinsa na neman tikitin tsayawa takarar shugabancin ya godema shugabannin jam’iyyar akan yadda aka tafiyar da zaben sharar fage na kujerar gwamnan Ekiti, sannan kuma ya bukaci maimaici a na Osun.

Zaben fid da gwani na PDP: Ko nayi nasara ko kada nayi nasara ina tare da PDP – Atiku Abubakar

Zaben fid da gwani na PDP: Ko nayi nasara ko kada nayi nasara ina tare da PDP – Atiku Abubakar

Ya jadadda cewa zaben fid da gwani na adalci zai bunkasa yiwuwar cin zaben jam’iyyar sannan kuma zai taimakawa PDP wajen dawo da martabarta da ta rasa.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Wani Sanata da ya hau kujerar mukami sau uku, Bukar Abba Ibrahim yace a shirye yake ya kara da Gwamna Ibrahim Gaidam wajen neman kujerar sanatan Yobe maso gabas a 2019.

KU KARANTA KUMA: Labari mai dadi: Jiragen ruwa 34 cike da man fetur, abinci da sauran kayayyakin amfani na shirin isowa Lagas

Jaridar Daiy Trust ta rahoto cewa gwamnan wanda ya fito daga mazaba daya da Sanata Ibrahim, na da kudirin takarar neman wannan kujera a majalisar wakilai.

Da yake jawabi ga manema labarai Bukar yace zai sake neman wannan kujera a zaben 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel