Yan gudun hijira dake shirin komawa jihohinsu sun je Unity Fountain Abuja domin yin godiya ga Buhari da rundunar soji

Yan gudun hijira da dama sun mamaye Unity Fountain a Abuja a shirye-shirye da suke na komawa jihohinsu daban-daban a arewa maso gabashin Najeriya.

Yan gudun hijiran da suka zamo marasa galihu sakamakon ayyukan yan ta’addan Boko Haram, sun shirya komawa mahaifarsu daga Kuchingoro dake Abuja da sauran yankunan dake babban birnin tarayya.

Mutanen wanda suka yada zango a Abuja na tsawon shekaru da dama sun isa Unity Fountain domin nuna godiya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da rundunar sojin Najeriya bisa kokarin da suka yi wajen yakar Boko Haram a yankin arewa maso gabas.

Yan gudun hijira dake shirin komawa jihohinsu sun je Unity Fountain Abuja domin yin godiya ga Buhari da rundunar soji

Yan gudun hijira dake shirin komawa jihohinsu sun je Unity Fountain Abuja domin yin godiya ga Buhari da rundunar soji

Daya daga cikin yan gudun hijiran Maryam Nuhu wacce tayi Magana a wajen gangamin ta bukaci hukumomi da su nemo wadanda suke ta daukar nauyin yan ta’addan Boko Haram domin hargitsa kasar.

Ta yaba ma shugaban hafsan soji, Laftanal Janar Tukur Buratai bisa namijin kokari da yayi wajen ganin abubuwa sun daidaita ta fannin tsaro.

Karin hotuna daga gangamin:

Yan gudun hijira dake shirin komawa jihohinsu sun je Unity Fountain Abuja domin yin godiya ga Buhari da rundunar soji

Yan gudun hijira dake shirin komawa jihohinsu sun je Unity Fountain Abuja domin yin godiya ga Buhari da rundunar soji

Yan gudun hijira dake shirin komawa jihohinsu sun je Unity Fountain Abuja domin yin godiya ga Buhari da rundunar soji

Yan gudun hijira dake shirin komawa jihohinsu sun je Unity Fountain Abuja domin yin godiya ga Buhari da rundunar soji

Yan gudun hijira dake shirin komawa jihohinsu sun je Unity Fountain Abuja domin yin godiya ga Buhari da rundunar soji

Yan gudun hijira dake shirin komawa jihohinsu sun je Unity Fountain Abuja domin yin godiya ga Buhari da rundunar soji

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel