N5m ga duk wanda ya gano inda ake kera bam a cikin birnin Maiduguri, inji Hafsan soji

N5m ga duk wanda ya gano inda ake kera bam a cikin birnin Maiduguri, inji Hafsan soji

- Janar Nikolas ya sanar jiya cewa zai bada ladan N5,000,000 ga duk wanda ya tona Boko Haram

- An gano lallai suna hada bam a cikin garin Maiduguri

- Kowa na tsoron tonawa, wadansu kuma sukan kare sojojin

N5m ga duk wanda ya gano inda ake kera bam a cikin birnin Maiduguri, inji Hafsan soji

N5m ga duk wanda ya gano inda ake kera bam a cikin birnin Maiduguri, inji Hafsan soji

A taron jin bahasi da bin diddigi kan matakan tsaro da ake bi a jihohin da ake yaki, Yobe, Borno da Adamawa, Janar Nicholas, mai tafiyar da tiyatar hadakar jami'an tsaron kasashen yankin, ya sanar da bada ladan N5,000,000 ga duk wanda ya tona Boko Haram.

Duk wanda ya gano inda ake hada bama-bamai dake fashe wa a birnin Maiduguri, da kewaye, yana da ladan kudi har N5m a hannu, muddin a tabbatar da bayanan nasa, inji JAnar din ga mazauna birnin.

Ya kuma kara da cewa, wannan na nufin ko a wasu birane ne aka kawo masa irin wadannan bayanan, mutum zai ci wannn lada.

DUBA WANNAN: An tafka asara a kasuwar hada-hadar hannayen jari

An dai sake samun karin mata masu kai hari cikin birnin, inda hukumomi ke da yaqinin lallai ba shigo da su ake daga wajen birnin ba, ba kuma shigo da bama-baman ake ba, don ko ta ina sun yi wa birnin kawanya.

Wannan na nufin lallai akwai wasu dake baiwa Boko Haramun din mafaka a cikin birnin, kuma hakan na nuna akwai yiwuwar sake ci gaba da samun hakan kafin a ballo jirgin.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel