Direban bankaura ya fuskanci hukuncin kisa bayan ya kade wani mutumi har lahira

Direban bankaura ya fuskanci hukuncin kisa bayan ya kade wani mutumi har lahira

Wani Direban bankaura mai shekaru 64, Usman Akewushola ya bankade wani mutumi da bai ji ba, bai gani ba a jihar Legas, wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar bawan Allah, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

Sai dai majiyar Legit.ng ta ruwaito a yayin da Yansanda suka tasa keyar Direban zuwaa gaban Kotu, inda ya fahimci yana fuskantar hukuncin kisa ne, sai fara zare ido yana magiya ga Kotu tare da neman sassauci.

KU KARANTA: Dakarun SARS sun cika hannu da wasu masu garkuwa da mutane dake amfani da kayan Yansanda

A ranar Juma’a, 22 ga watan Yuni ne aka gurfanar da Usman gaban Kotu kan tuhumarsa da ake yi da kashe wani mutumi mai suna Joseph Nnabor sakamakon tukin ganganci da yake da kuma gudun wuce iri.

Dansanda mai shigar da kara, Sajan Raphael Donny ya shaida ma Kotu cewa a ranar 9 ga watan Yuni ne Usman a kade mutane biyu yayin da yake tukin ganganci a tashar Mota ta Obadeyi dake unguwar Ijaiye na jihar Legas.

Dansanda Donny yace Usman na tuka wata mota kirar Toyota ce a lokacin da ya bankade mutanen, inda nan take guda daga cikin mutanen biyu, Joseph, ya fadi matacce, yayin da gudan ya samu rauni, wanda a yanzu haka yana Asibiti.

Wani karin laifi a cewar Dansandan yayin da dayake tsatstsage ma Kotu jawabi shi ne, Direban ya tsere bayan ya kade mutanen, inda yace da kyar da sudin goshi jama’a suka yi masa tara tara suka kama shi, suka lakada masa dan banzan duka.

Majiyarmu ta ruwaito laifin da ake tuhumar Direban da shi ya saba ma sashi na 18 da na 20 na dokokin tuki a jihar Legas, wanda ka iya tabbatar da hukuncin kisa akansa. Sai dai Direban ya musanta tuhumar da ake masa.

Bayan sauraron dukkanin bangarorin biyu, Alkalin Kotun, mai shari’a A Adebayo ya bada belin wanda ake kara akan kudi naira miliyan daya, tare da mutane biyu da zasu tsaya masa, suma akan kudi naira miliyan kowanne, sa’annan ta dage sauraron karar zuwa ranar 16 ga watan Yuli.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel