Yanzu Yanzu: Hukumar DSS ta kama Sanata Enyinnaya Abaribe

Yanzu Yanzu: Hukumar DSS ta kama Sanata Enyinnaya Abaribe

Hukumar yan sandan farin kaya (DSS) ta kama Sanata mai wakiltan yankin Abia ta Kudu a majalisar dattawa, Sanata Eyinnaya Abaribe.

An kama shi ne a wani shahararren otel dake yankin Maitama a babban birnin tarayya Abuja, a ranar Juma’a, 22 ga watan Yuni.

Abaribe tsohon mataimakin gwamnan jihar Abia, ya kasance babban dan adawan gwamnatin shugaba Buhari.

Yanzu Yanzu: Hukumar DSS ta kama Sanata Enyinnaya Abaribe

Yanzu Yanzu: Hukumar DSS ta kama Sanata Enyinnaya Abaribe

Zuwa yanzu dai babu wani cikakken bayani akan dalilin kamun nashi.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Jami’an yan sandan farin kasa wato DSS sun kama tsohon gwamnan jihar Benue, Mista Gabriel Suswam, kan lamuran tsaro a jihar.

KU KARANTA KUMA: Kasafin 2018: Da shugaba Buhari ya sani bai sanya hannu akai ba – Sanata Shehu Sani

An kama tsohon gwamnan ne bayan gwamna mai ci, Mista Samuel Ortom ya aika wasika ga hukumar DSS kan lamarin tsaro a jihar inda ake zargin Suswam da shirin lalata gwamnatin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel