Labari mai dadi: Jiragen ruwa 34 cike da man fetur, abinci da sauran kayayyakin amfani na shirin isowa Lagas

Labari mai dadi: Jiragen ruwa 34 cike da man fetur, abinci da sauran kayayyakin amfani na shirin isowa Lagas

Akalla jiragen ruwa 34 cike da kayan man fetur, abinci da sauran kayayyakin amfani ake sanya ran isowarsu tashoshin jirgin ruwa na Apapa da Tin Can Island Ports daga ranar Juma’a, 30 ga watan Yuni inji hukumar tashoshin jiragen ruwa na Najeriya (NPA).

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa akalla shida daga cikin jiragen 34 na dauke da man fetur, yayinda sauran 25 ke dauke da alkama, mai, kwantenan kayyayaki, daskararen kifi, waken suya, taki, da kuma karafuna.

Labari mai dadi: Jiragen ruwa 34 cike da man fetur, abinci da sauran kayyayakin amfani na shirin isowa Lagas

Labari mai dadi: Jiragen ruwa 34 cike da man fetur, abinci da sauran kayyayakin amfani na shirin isowa Lagas

Sannan kuma sauran jiragen uku zasu kasance dauke da man diesel, da kuma gas.

KU KARANTA KUMA: Kasafin 2018: Da shugaba Buhari ya sani bai sanya hannu akai ba – Sanata Shehu Sani

A cewar hukumar ta NPA, tuni takwas daga cikin jiragen sun isa tashoshin jiragen ruwan cike da taki, man jirgi, diesel da kuma fetur.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel