Yan sanda sun damke yan Shi’a 42 masu alaka da kisan dan sanda a Kaduna

Yan sanda sun damke yan Shi’a 42 masu alaka da kisan dan sanda a Kaduna

Hukumar yan sandan Najeriya a jihar Kaduna ta damke mambobin kungiyar Shi’a 42 tattare da kisan wani jami’in dan sanda a jiya Alhamis, 21 ga watan Yuni a jihar Kaduna.

Kakakin hukumar yan sanda, Mukhtar Aliyu, ya bayyana wannan kamu ne a yau Juma’a, 22 ga watan Yuni a jihar Kaduna.

Ya ce lallai za’a gurfanar da wadannan mutane 42 muddin an kammala bincike a kan su.

Damke wadannan yan Shi’a ya faru ne bayan rikici ya barke tsakanin jami’an yan sanda da yan kungiyar Shi’a masu zanga-zangar cigaba da tsare shugabansu kuma malaminsu, Sheik Ibrahim Zakzaky.

KU KARANTA: Jami'an SARS na bogi sun shiga hannu

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa an hallaka dan sanda daya har lahira a sabuwar rikici da ya barke tsakanin yan sanda da yan kungiyar Shi'a a zanga-zangan da sukeyi kan cigaba da tsare shugabansu, Sheik Ibrahim Zakzaky.

Kakakin hukumar yan sanda a jihar Kaduna, Muktar Aliyu, ya tabbatar da wannan labari da ya faru a yau Alhamis, 1 ga watan Yuni 2018.

Game da cewarsa, dan sandan na tafiyarsa a kan hanya kawai sai yyan Shi'an sukayi masa ribiti da caccaka masa wuka har lahira.

Sheikh Ibrahim El-Zakzaky dai yana gurfana a kotu ne kan laifin tara mabiya ba bisa doka ba, kokarin fito-na-fito da gwamnati.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel