Ziyarar Atiku Bayelsa: Jam'iyyar PDP a jihar ta kwance masa zane a kasuwa

Ziyarar Atiku Bayelsa: Jam'iyyar PDP a jihar ta kwance masa zane a kasuwa

Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya ta Peoples Democratic Party, PDP kuma jam'iyya mai mulki a jihar ta Bayelsa ta fito ta nisanta kanta da mai neman tikin takarar shugabancin kasar nan a karkashin jam'iyyar, Atiku Abubakar.

Jam'iyyar reshen jihar dai ta bayyana cewa ita har yanzu bata riga ta yanke shawarar wanda zata goyawa baya ba a cikin 'yan takarar dake neman tikitin jam'iyyar a zaben 2019 mai zuwa.

Ziyarar Atiku Bayelsa: Jam'iyyar PDP a jihar ta kwance masa zane a kasuwa

Ziyarar Atiku Bayelsa: Jam'iyyar PDP a jihar ta kwance masa zane a kasuwa

KU KARANTA: Ayyuka 5 da majalisa ta zaftarewa kudi a kasafin 2019

Legit.ng ta samu cewa jam'iyyar ta ce yin wannan bayanin ya zama dole ne biyo bayan wasu 'yan maganganu da suke ji suna yawa a gari bayan ziyarar da dan takarar yakai a jihar.

A wani labarin kuma, Kamar dai yadda muka samu daga majiyoyin mu, yanzu haka dai 'yan majalisa da dama na tarayya na cike da bakin ciki da haushin shugabannin su kan yadda suka kasafta cushen kudin da suka yi wa kasafin kudin 2018.

Mun samu cewa 'yan majalisar wadan da suka ce sam basu ji dadin yadda rabon ya kasance ba sun ce yayin da shugabannin majalisar suka rabawa kansu ayyukan da suka kai na Naira biliyan daya, sauran kuma sun tashi ne da ayyukan kasa da Naira miliyan 50 kacal.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel