Rigima a kwance majalisa kan yadda aka kasafta cushen Naira biliyan 578 a kasafin kudin 2018

Rigima a kwance majalisa kan yadda aka kasafta cushen Naira biliyan 578 a kasafin kudin 2018

Kamar dai yadda muka samu daga majiyoyin mu, yanzu haka dai 'yan majalisa da dama na tarayya na cike da bakin ciki da haushin shugabannin su kan yadda suka kasafta cushen kudin da suka yi wa kasafin kudin 2018.

Mun samu cewa 'yan majalisar wadan da suka ce sam basu ji dadin yadda rabon ya kasance ba sun ce yayin da shugabannin majalisar suka rabawa kansu ayyukan da suka kai na Naira biliyan daya, sauran kuma sun tashi ne da ayyukan kasa da Naira miliyan 50 kacal.

Rigima a kwance majalisa kan yadda aka kasafta cushen Naira biliyan 578 a kasafin kudin 2018

Rigima a kwance majalisa kan yadda aka kasafta cushen Naira biliyan 578 a kasafin kudin 2018

KU KARANTA: Nima dan Tijjaniyya ne - Buhari

A don haka ne ma suka sha alwashin cewa da zarar an dawo zaman majalisar za su tayar da kayar baya su kuma yi gumurzu domin ganin sun kwatowa kan su 'yancin su.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya koka akan yadda majalisar tayi masa cushen ayyuka tare da rage kudaden ayyukan da ya shirya yi lokacin da ya tarrafawa kasafin kudin hannu.

A wani labarin kuma, Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya ta Peoples Democratic Party, PDP kuma jam'iyya mai mulki a jihar ta Bayelsa ta fito ta nisanta kanta da mai neman tikin takarar shugabancin kasar nan a karkashin jam'iyyar, Atiku Abubakar.

Jam'iyyar reshen jihar dai ta bayyana cewa ita har yanzu bata riga ta yanke shawarar wanda zata goyawa baya ba a cikin 'yan takarar dake neman tikitin jam'iyyar a zaben 2019 mai zuwa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel