Mu na goyon bayan sauya Fasalin 'Kasa - Osinbajo

Mu na goyon bayan sauya Fasalin 'Kasa - Osinbajo

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa, gwamnatin su ta yanzu ba ta adawa ko hammaya da sauya fasalin kasa sabanin yadda mafi akasarin al'ummar kasar nan suka dauka.

Yake cewa gwamnatin sa tana goyon bayan duk wani nau'i na sauya fasalin kasa da zai amfani al'ummar Najeriya.

Osinbajo ya bayyana hakan ne yayin ganawa da Sarakunan gargajiya na jihar Ekiti a fadar Sarki Ewi na Ado-Ekiti, Oba Rufus a ranar Larabar da ta gabata.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya bayyana, Kakakin Mataimakin Shugaban Kasa Mista Laolu Akande, ya gabatar da cikakkun jawaban Ubangidan sa ga manema labarai a ranar Alhamis din da ta gabata.

Mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa ba bu abinda 'yan Najeriya suka fi bukata a halin yanzu kamar zaman lafiya a kwanciyar hankali.

Mu na goyon bayan sauya Fasalin 'Kasa - Osinbajo

Mu na goyon bayan sauya Fasalin 'Kasa - Osinbajo

Ya caccaki wadanda ke samun gamsuwa wajen sanya kabilanci ko addini cikin siyasa domin raba kawunan al'ummar kasar nan.

Osinbajo ya ci gaba da cewa, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dukufa wajen tabbatar da ci gaba cikin kowace jiha a kasar nan ba tare da la'akari da jam'iyyar siyasa dake jagoranci a jihar ba.

KARANTA KUMA: Kada ku damu da Kidahumancin nPDP - Adamu ga APC

A sanadiyar haka ne ya sanya jihar Ekiti ke ci gaba da amfanuwa da shirin gwamnatin tarayya na samar da sana'o'i duk da kasancewar tana karkashin jagorancin jam'iyyar adawa ta PDP.

Ya hikaito yadda shirin N-Power ya samar da abin yi ga matasan jihar Ekiti 3,339 da a yanzu ya rage ma su zaman kashe wando.

Y kara da cewa, wadanda suke amfana da shirin N-Power su na ci gaba da taimakawa jihar wajen koyarwa a makarantu, harkokin noma da kuma ma'aikatun lafiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel