Kasafin 2018: Da shugaba Buhari ya sani bai sanya hannu akai ba – Sanata Shehu Sani

Kasafin 2018: Da shugaba Buhari ya sani bai sanya hannu akai ba – Sanata Shehu Sani

Sanatan jam’iyyar Progressives Congress (APC), Shehu Sani, yace bai kamata ace shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kasafin kudin 2018 ba.

Sani na maida martani ne ga korafin da shugaban kasar yayi akan cewa majalisar dokoki sun zaftare kasafin, wanda zai shafi manyan ayyuka da dama.

Sanatan mai wakiltan yankin Kaduna ta tsakiya a majalisar dokokin yace sanya hannun da shugaban kasar yayi akan takardun ya nuna amincewarsa.

Kasafin 2018: Da shugaba Buhari ya sani bai sanya hannu akai ba – Sanata Shehu Sani

Kasafin 2018: Da shugaba Buhari ya sani bai sanya hannu akai ba – Sanata Shehu Sani

Sanatan ya wallafa wannan kalami ne a shafinsa na twitter.

KU KARANTA KUMA: Yan sanda sun kama ýan Shi’a 9 a Kaduna

Idan bazaku manta ba shugaba Buhari wanda ya sanya hannu akan kasafin 2018 a ranar Laraba, 20 ga watan Yuni ya bayyana cewa majaisar dokoki ta yi ragi na kimanin naira biliyan 347 wanda za’a yi amfani das u waje aiwatar da ayyuka 4,700.

Ya kuma bayyana cewa sun sanya ayyuka 6,403, wanda ya kai naira biliyan 578 inda hakan zai shafi wasu manyan ayyuka.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel