Zamu daina shigo mai nan zuwa 2019 – Maikanti Baru

Zamu daina shigo mai nan zuwa 2019 – Maikanti Baru

Nan zuwa 2019, Najeriya ta zange dantse wajen daina shigo da man fetur daga kasashen waje da kuma fara fitar da shi, shugaban kamfanin man feturin Najeriya NNPC, Dr Maikanti Baru, ya bayyana haka.

Yayinda yake jawabi a taron kasashe masu fitar da mai wato OPEC a Vienna, kasar Austria, Baru ya laburtawa mahalarta taron cewa tunanin da ake wa Najeriya a da ya canza tunda wannan gwamnati ta hau karagar mulki.

Yace: “Manufarmu shine mu fara fitar da kayan man fetur a shekarar 2019. Wannan na cikin abubuwan da muke tattaunawa na farfado da matatun man fetur 4 da suke da shi.”

“Wannan wani sabon salo ne na sanya hannun jari kuma zai zama tushen canza yadda ake gudanar da kasuwanci a Najeriya.”

Zamu daina shigo mai nan zuwa 2019 – Maikanti Baru

Zamu daina shigo mai nan zuwa 2019 – Maikanti Baru

Ya kara da cewa gwamnatin Najeriya ta sanyaya yanayin kasuwanci domin masu sanya hannun jari su ji dadi ku da dama daga cikinsu sun yi amfani da wannan garabasa.

A bangaren iskar gas kuma, Baru yace: “Samuwar iskar gas a kasuwa ya ninku ninki uku daga 500mmscf/d a 2010 zuwa 1500mmscf/d a yanzu. Mun kammala sabon dogon layi bututun main a kilometer 600km.”

KU KARANTA: Deleget 6800 ne zasu halarci taron APC

A bangare guda, ministan man fetur, Emmanuel Ibe Kachikwu, a jiya ya nuna rashin yardarsa da kara yawan fitar da man fetur.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel