Deleget 6,800 ne za suyi zabe a taron gangamin jam’iyyar APC gobe

Deleget 6,800 ne za suyi zabe a taron gangamin jam’iyyar APC gobe

Akalla deleget 6,800 ake sa ran za su kada kuriarsu a zaben taron gangamin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da za’a gudanr gobe Asabar, 23 ga watan Yuni, 2018 inda za su zabi sabbin shugabannin jam’iyyar.

Shugaban karamin kwamitin yada labaran kwamitin shirya taron gangamin, gwana Abiola Ajimobi, ya bayyana hakan a ranan Alhamis, 21 ga watan Yuni.

Kana tsohon gwamnan jihar Zamfara, Sanata Ahmed Yarima, wanda shine shugaban kwamitin kan tantance yan takara ya ce kwamitin ta fara tantance deleget daga jihohi 36 a fadin tarayya.

Deleget 6,800 ne za suyi zabe a taron gangamin jam’iyyar APC gobe

Deleget 6,800 ne za suyi zabe a taron gangamin jam’iyyar APC gobe

Ya bada tabbacin cewa za’a tantance deleget sosai kafin a bari wani ya shiga farfajiyar Eagle Square ranan Asabar.

“Zamu sanya lamba saboda da mutum ya shigo ciki, za’a gane shi waye, sannan tantance shi, sannan ya samu shiga.”

“Ko a wajen kada kuri’a a ciki, za’a ba da wani kati daban kafin a yarda mutum ya kuri’a”.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel