Ai da ka dawo mana da kasafin kudin tunda baka amince da gyarar da mu kayi ba- Melaye ya fadawa Buhari

Ai da ka dawo mana da kasafin kudin tunda baka amince da gyarar da mu kayi ba- Melaye ya fadawa Buhari

Dino Melaye, sanata mai wakiltar kogi ta yamma ya ce shugaba Muhammadu Buhari yana da damar mayar da kasafin kudin 2018 ga majalisa idan bai gamsu da irin gyaran da su kayi ba.

A ranar Laraba ne dai shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kan kasafin kudin. Sai dai ya ce akwai abubuwan da majalisar su ka kara cikin kasafin kudin da bai gamsu da su ba.

Shugaban kasan ya ce 'yan majalisan sun kara ayyuka guda 6,043 hakan kuma ya kasafin kudin ya karu da naira 14.5 biliyan.

'Ai da ka dawowa majalisa da kasafin kudin' - Melaye ya fadawa Buhari

'Ai da ka dawowa majalisa da kasafin kudin' - Melaye ya fadawa Buhari

KU KARANTA: Sharri ake masa, Buhari bashi da hannu cikin kashe-kashen Benue - Matasan Benue

Ya kuma ce sun rage kudaden wasu ayyuka amma dai ya rattaba hannu a kan kasafin kudin ne saboda a fara gudanar da ayyuka a kasar kuma tattalin arzikin ya cigaba da habaka.

A martaninsa, Dino Melaye ya zargi shugaba Muhammadu Buhari da yunkurin shafawa majalisa kashin kaza a idanun talakawa.

Ya ce dama aikin majalisar shine tattance kasafin kudin da shugaban kasan ya kawo tare da yin gyare-gyare a wuraren da suka dace.

"Fadar shugaban kasa ba ta da ikon dakile ikon da doka ya bawa majalisa. Majalisar bangare ce zaman kanta.

"Idan shugaban kasa bai gamsu da gyare-gyaren da mu kayi ba, yana da damar ya dawo mana da kasafin kudin tare da bayyana wuraren da bai amince da su ba." inji Melaye.

A wata labarin Legit.ng ta kawo muku cewa mutum daya ne ya yi saura cikin masu takarar shugabancin jam'iyyar APC, dukkan sauran sun janye sun bar tsohon gwamnan Jihar Edo, Adams Oshiomole.

Dama galibin jiga-jigan jam'iyyar ta APC da ma shugaba Muhammadu Buhari sun nuna goyon bayansu ga Mista Oshiomole.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel