Dakarun Sojin Najeriya sun hallaka yan Boko Haram 35, sun kashe 25

Dakarun Sojin Najeriya sun hallaka yan Boko Haram 35, sun kashe 25

Dakarun rundunar mayakan Sojin kasa ta Najeriya sun samu nasarar kashe mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram dake kai harin kunar bakin wake su Talatin da biyar, tare da kama guda Ashirin da biyar daga cikinsu, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito babban kwamandan yaki da Boko Haram, Manjo Janar Nicholas Rogers ne ya bayyana haka a ranar Alhamis, 21 ga watan Yuni a yayin wata ganawa da manema labaru a garin Maiduguri, inda ya nemi jama’an gari da yan kato da gora su dage wajen gano inda ake hada bamabamai.

KU KARANTA: Babban labari: Abubuwa guda 3 da suka taba sanya Buhari fashewa da kuka

“Ina da tabbacin a yankinan yan Boko Haram ke hada Bamabamansu, don haka nake kira ga jama’a da su taimaka mana da bayanai game da duk wani waje da Boko Haram ke amfani da shi wajen hada Bom a garuruwan Borno, Adamawa da Yobe, ni kuma na yi alkawarin bada tukuwicin naira miliyan biyar ga duk wanda ya bamu bayani.” Inji shi.

Dakarun Sojin Najeriya sun hallaka yan Boko Haram 35, sun kashe 25

Rogers

Rogers ya yaba ma dakarun Sojin Najeriya, inda yace tun bayan darerwarsa mukamin babban kwamanda kimanin shekara daya data gabata, Sojoji sun kama yan kunar bakin wake guda 25 tare da kashe 35 a Maiduguri, Konduga, Bama, Damboa, Mubi da Magagali, da kuma wasu sassan jihar Yobe.

Daga karshe Kwamanda Rogers ya jinjina kokarin da Sojoji keyi a yaki da suke yi da yan ta’adda, inda yace a hakan ne yayi sanadiyyar bude manyan hanyoyi da tituna da suka kwashe shekara da shekaru suna rufe.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel