Kashe kashe a Zamfara: Gwamnatin Buhari ta caccaki gwamna Abdul Aziz Yari

Kashe kashe a Zamfara: Gwamnatin Buhari ta caccaki gwamna Abdul Aziz Yari

Gwamnatin tarayya ta danganta kashe kashen da ake yi a jihar Zamfara ga rashin kwarewa da sanin makaman aiki akan sha’anin mulki na gwamnan jihar, Abdul Aziz Yari, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Ministan cikin gidan, Abdulrahman Dambazau ne ya bayyana haka a ranar Alhamis, 21 ga watan Yuni, yayin wani babban taron yan jaridu na Duniya daya gudana a fadar shugaban kasa, inda yace gwamnan baya gudanar da aikinsa a matsayinsa na babban mai kare rai da dukiyoyin al’ummarsa.

KU KARANTA: Kuma dai: an kwashi gawarwakin mutane 4 bayan da yan bindiga suka kai hari jihar Filato

Ministan yace kyakkyawar mulki ne kadai zai kawo karshen kashe kashen da ake yi a jihar Zamfara, tare da maido da dawamammen zaman lafiya, ya kara da cewa idan za’a baiwa Yari dukkanin Sojojin Duniya ba zai iya magance matsalar ba.

“Ba daidai bane a matsayinka na gwamnan jaha kace ka wancakalar da aikinka na babban jami’in tsaron al’ummarsa, wannan na nuni kadai da rashin kwarewa da sanin aiki a sha’anin mulki, Alhali kwarewar ake bukata wajen magance matsalar.” Inji shi.

Daga karshe Dambazau yace gwamnatin tarayya zata fara rajistan dukkanin bakin haure da suka dade a Najeriya, don ta dinga lura da shige da ficensu, haka zalika ma’aikatan cikin gida ta samar da wata cibiya na musamman da zata dinga lura da shige da fice a iyakokin Najeriya

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel