Jam'iyyar PDP ta gargadi Gwamnatin Tarayya kan Yankunan Kiwon Shanu

Jam'iyyar PDP ta gargadi Gwamnatin Tarayya kan Yankunan Kiwon Shanu

Jam'iyyar adawa ta PDP ta gargadi gwamnatin tarayya akan ta tabbata da ta yi taka tsantsan yayin gudanar da shiri da tsare-tsaren ta na kafa yankuna na garken shanu cikin wasu sassa a fadin kasar nan.

Yayin bayyana cewa kasar Najeriya ta kasance cikin wasu lokuta masu hadari, jam'iyyar ta gargadi gwamnatin akan ta zurfafa bincike gami da tuntube-tuntube na neman shawarwari akan lamarin domin gujewa ta'azzara matsalolin da ta ke ikirarin magancewa a halin yanzu.

Jam'iyyar ta PDP ta lura da cewa a halin yanzu an fara samun rashin jituwa kan lamarin a tsakanin manyan masu ruwa da tsaki, kungiyoyi da wasu jihohi a fadin kasar musamman kudaden da za a batar da kuma mallakar yankunan yayin samar da garkunan kiwon shanu.

Jam'iyyar PDP ta gargadi Gwamnatin Tarayya kan Yankunan Kiwon Shanu

Jam'iyyar PDP ta gargadi Gwamnatin Tarayya kan Yankunan Kiwon Shanu

Yayin ganawa da manema labarai a babban birnin kasar nan a ranar Alhamis din da ta gabata, Kakakin jam'iyyar Mista Kola Ologbondiyan ya bayyana cewa, jam'iyyar ta damu musamman dangane da rashin tuntube-tuntube daga bangaren gwamnatin tarayya kan tsare-tsaren da ta shifida da a yanzu ya fara janyo rashin daidaito musamman a tsakanin wasu mabambanta kabilu.

Jam'iyyar ta kuma gargadi gwamnatin tarayya akan tabbatar da kiyaye duk wasu dokoki da tsare-tsare da kudin tsarin mulkin kasa ya shimfida domin kawar da rashin daidaito da jituwa a tsakankanin al'umma.

KARANTA KUMA: An ceto fiye da Mutane Miliyan 1 daga hannun 'Yan Boko Haram cikin watanni Shida - Hukumar Soji

Hakazalika jam'iyyar ta kara da cewa, kasar nan ta fuskanci rashin jituwa, rikici, tayar da kayar baya, zubar jina da ya kamata a dauki tsauraran matakai domin magance matsalolin da sun kai intaha a kasar nan.

A yayin haka kuma jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, jam'iyyar ba ta gushe ba akan matsayar ta na zargin cewar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari tana nan kan batun ta na kafa kahon zuka akan shugabannin jam'iyyun adawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel