Da dumin sa: Tsohon ministan ayyuka a lokacin Sardauna ya rasu yana da shekaru 93

Da dumin sa: Tsohon ministan ayyuka a lokacin Sardauna ya rasu yana da shekaru 93

Labarin da muke samu da dumin sa yanzu yana nuna mana cewa tsohon ministan ayyuka a jamhuriya ta farko a Najeriya lokacin su Sardauna mai suna Sule Gaya ya rasu.

Kamar dai yadda muka samu daga majiyar mu ta Daily Nigerian, daya daga cikin 'ya'yan mamacin Binta Gaya ta ce ya rasu ne da yammacin ranar Alhamis 21 ga watan Yuni yana da shekaru 93 a duniya.

Da dumin sa: Tsohon ministan ayyuka a lokacin Sardauna ya rasu yana da shekaru 93

Da dumin sa: Tsohon ministan ayyuka a lokacin Sardauna ya rasu yana da shekaru 93

KU KARANTA: Manyan ayyukan Buhari 5 da majalisa suka ragewa kudi

Legit.ng ta samu cewa an haifi marigayin ne dai a garin Gaya, cikin karamar hukumar Gaya ta jihar a Kano a shekarar 1925.

Alhaji Gaya dai da ke zaman shahararren dan siyasa an zabe shi ne a majalisar dokoki a wancan lokacin kafin daga baya ya zama Sakataren majalisar.

Daga baya ne kuma ya rike ma'aikatar ilimi ta jihar Kano sannan kuma aka nada shi sarautar Sarkin Fadan Kano.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel