Zaben 2019: Za'a yi anfani da jiragen yaki wajen raba kayayyakin zabe a Najeriya

Zaben 2019: Za'a yi anfani da jiragen yaki wajen raba kayayyakin zabe a Najeriya

Babban hafsan rundunar sojin saman Najeriya Air Marshal Sadique Abubakar ya bayyana cewa rundunar a shirye take da ta taimakawa hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC wajen rabon kayayyakin zaben 2019 mai zuwa.

Mista Abubakar ya bayyana hakan ne a garin Abuja yayin da yake gabatar da jawabin sa ga kwamandojin rundunar a garin Abuja.

Zaben 2019: Za'a yi anfani da jiragen yaki wajen raba kayayyakin zabe a Najeriya

Zaben 2019: Za'a yi anfani da jiragen yaki wajen raba kayayyakin zabe a Najeriya

KU KARANTA: Nima dan Tijjaniyya ne - Buhari

Legit.ng ta samu cewa sai dai hafsan sojojin yace za su yi hakan ne kawai idan hukumar ta zabe ta bukaci hakan yana mai jan hankalin su da kar su kuskura su shiga harkokin siyasa.

A wani labarin kuma, Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma mai neman takarar shugabancin kasar nan Alhaji Atiku Abubakar ya yabawa tsohon shugaban kasar nan Goodluck Jonathan tare da fada masa cewa tarihi ba zai taba mantawa da shi ba.

Mun samu cewa Atiku ya bayyana hakan ne a yayi wata ziyarar ban girma da ya kaiwa tsohon mataimakin shugaban kasar a gidan sa dake a jihar Bayelsa ranar Larabar da ta gabata.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel