Zamu saka Fayose a akurki ranar zaben gwamna a jihar Ekiti – Dan takarar APC

Zamu saka Fayose a akurki ranar zaben gwamna a jihar Ekiti – Dan takarar APC

Dan takarar jam’iyyar APC a zaben gwamnan Ekiti mai zuwa, Kayode Fayemi, ya tabbatar wa magoya bayan sa cewar, za a samar da tsaro ranar zaben gwamnan jihar da za a yi 14 ga watan gobe na Yuli.

Fayemi ya yi kira ga masu kada kuri’a das u fito su kada kuri’un su cikin kwanciyar hankali ba tare da fargabar gamuwa da kowanne irin tashin hankali ba kamar yadda gwamnan jihar, Ayo Fayose, ke yi masu barazana ba.

Zamu saka Fayose a akurki ranar zaben gwamna a jihar Ekiti – Dan takarar APC

Fayose da Fayemi

Dan takarar na jam’iyyar APC ya shaidawa jama’ar da suka halarci taron yakin neman zaben sa na yau, Alhamis, cewar, shi kan sa gwamna Fayose a akurki zasu saka shi ranar da zarar ya kada kuri’ar sa a mazabar sa.

DUBA WANNAN: Bashi da wani tasiri a siyasar Kano – Ganduje ya yi tone-tone a kan rikicin sa da Kwankwaso

Zamu tabbatar an samu tsaro domin bawa masu kada kuri’a dammar yin zabe ba tare da wata fargaba ko tsoron samun barkewar rikici ba. Za a yi zabe mai tsafta cikin kwanciyar hankali,” a cewar Fayemi.

Fayemi na wadannan kalamai ne ga jama’ar mazabar kananan hukumomin Ido/Osi inda ya ziyarta a yau, Alhamis, a cigaba day akin neman zaben sa da ya ke yi a jihar ta Ekiti.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel