Inganta aikin jarida na kawo gyara a harkokin gwamnati - Shugaba Buhari

Inganta aikin jarida na kawo gyara a harkokin gwamnati - Shugaba Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kira ga 'yan jarida a fadin duniya da su rika gudanar da ayyukansu kamar yadda dokan aikin ta tanada tare da bayar da sahihan rahotanni.

A cewarsa hakan na da matukar muhimmanci wajen cigaban kasa kuma hakan zai kare yaduwar labarai na karya da suka cika wasu kafafen yadda labaran.

Inganta aikin jarida na kawo gyara a harkokin gwamnati - Shugaba Buhari

Inganta aikin jarida na kawo gyara a harkokin gwamnati - Shugaba Buhari

Shugaban kasan ya yi wannan kiran ne a taron yan jarida na duniya ta shekarar 2018 wanda ake yiwa taken 'Dalilin da yasa aikin jarida mai kyau ke da muhimmanci' da akayi a ranar Alhamis a babban birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA: Sojin Sama sun ceto mutane uku daga hannun masu garkuwa da mutane a Zamfara

Ya ce, "A wannan zamanin da akwai wuya wajen banbance kalaman kiyaya da damar bayyana ra'ayi, aikin jarida mai kyau yana da matukar muhimmanci.

"A inda labaran karya ke rinjayar na ga gaskiya, aikin jarida na gari yana da muhimmanci. Aikin jarida na gari na kawo cigaba a gwamnati."

Hakan yasa shugaba Muhammadu Buhari ya yi kira ga mahallarta taron da suyi tunani sosai a kan taken ranar 'yan jaridar a yayin da suke tattaunawa.

Ya kuma mika godiyarsa da Cibiyar Jarida na kasa da kasa da bawa Najeriya damar daukan bakuncin taron da wannan shekarar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel