Kasafin 2018: Majalisar dokoki basu da tausayi suna da son kansu - Kungiya

Kasafin 2018: Majalisar dokoki basu da tausayi suna da son kansu - Kungiya

Kungiyar matasan Iyaw, IYC, ta bayyana zaftare kasafin 2018 da majalisar dokoki suka yi a matsayin gaban kansu sannan kuma cewa hakan ya sabawa ra’ayin al’umman kasar.

A wata sanarwa dauke da hannun shugaban kungiyar na kasa, Eric Omare, kungiyar tayi Allah wadai sa rage kudin da yan majalisun sukayi na muhimman ayyukan da za’a aiwatar da kuma aikin hanyar gabas maso yamma wanda ake ganin shine babban hanyar dorewar zaman lafiya a Niger Delta.

A cewar matasan, wannan mataki da majalisar dokokin ta dauka ya nuna cewa mambobinta basu da tausayi, tare da cewa yan majalisan sun nuna cewa basa kaunar cigaban mutane.

Kasafin 2018: Majalisar dokoki basu da tausayi suna da son kansu - Kungiya

Kasafin 2018: Majalisar dokoki basu da tausayi suna da son kansu - Kungiya

Ta kuma bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya daina bata lokaci wajen turawa majalisar dokoki kasafin kudi wanda zai zamo dama ga majalisar wajen canja ainahin dokar da aka tura masu.

KU KARANTA KUMA: Dalilin mu na kara kasafin kudin 2018 – Majalisar tarayya sun kare kansu

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaba Muhammadu Buhari a jiya yayin da yake sa hannu a kan kasafin kudin shekarar 2018 a fadar gwamnatin sa a bayyana cewa 'yan majalisar tarayya sun yi masa jagwalgwalo akan kasafin kudin da sunan dubawa.

Shugaban kasar dai ya bayyana cewa 'yan majalisar sun rage kudaden ayyukan sa da suka kai akalla sama da Naira biliyan 300 akan ayyuka sama da dubu 4 da ya kuduri aniyar yi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel