Hukumar 'Yan sanda ta yiwa jami'an ta 51 ado na ƙarin girma a jihar Katsina

Hukumar 'Yan sanda ta yiwa jami'an ta 51 ado na ƙarin girma a jihar Katsina

A ranar Alhamis din da ta gabata ne hukumar 'yan sanda reshen jihar Katsina ta yiwa jami'an ta 51 ado na ƙarin girma zuwa matamakai daban-daban da suka hadar da Manyan Sufirtanda, Sufirtanda, Mataimakan Sufirtanda da sauransu.

Da yake jawabi ga jami'an da aka yiwa ƙarin girma, kwamishinan 'yan sanda na jihar Muhammad Wakil, ya kalubalance su akan hada hannu da juna wajen tunkara da tare da magance matsalolin tsaro da kuma tabbatar da kiyaye doka a fadin jihar.

Babban jami'in ya kuma gargade su akan kada zu gaza wajen bayar da himma da kuma kwazo domin tabbatar da an magance matsalolin tsaro a fadin jihar.

Ya jaddada cewa yanayin tsaro cikin kasar nan a halin yanzu yana bukatar tsauraran matakai da za su magance miyagun laifuka irin su fashi da makami, rikicin makiyaya da manoma da kuma rikice-rikece na kabilanci da iyaka.

Legit.ng ta fahimci cewa, kwamishinan 'yan sanda ya kuma nemi jami'an akan sanya tsohon Mahaliccin su yayin sauke nauye-nauyen da rataya a wuyan su.

Hukumar 'Yan sanda ta yiwa jami'an ta 51 ado na ƙarin girma a jihar Katsina

Hukumar 'Yan sanda ta yiwa jami'an ta 51 ado na ƙarin girma a jihar Katsina

Hakazalika kwamshinan 'yan sanda yayin gargadin su akan jajircewa bisa aiki, ya kuma bayar da tabbacin sa da cewar hukumar ba za ta gaza wajen daukar matakan da zasu tabbatar da wanzuwar tsaro a jihar.

KARANTA KUMA: Dalilin da yasa aka taso 'Keyar 'yan Najeriya 34 daga Kasar Amurka

A yayin yabo ga hukumar 'yan sanda ta kasa da kuma Sufeto Janar na hukumar, Ibrahim K. Idris dangane da ƙarin girma ga jami'an, ya bayyana lurar sa da cewar makamancin wannan ƙarin girma shine karo na farko a tarihin jihar Katsina

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya bayyana, shugabannin hukumomin tsaro da dama na kasar nan sun halarci wannan taron biki na ƙarin girma da aka gudanar a cikin birnin na Katsinan Dikko.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel