Da duminsa: Shugaban kasa Buhari zai ziyarci Katsina gobe

Da duminsa: Shugaban kasa Buhari zai ziyarci Katsina gobe

- Bayan ziyarar da shugaba Buhari ya kai Bauchi yau gobe zai zarce Katsina don wata ziyarar

- Gwaman jihat Katsinan Aminu Bello Masari ne ya tabbatar da hakan

- Ziyarar zuwa Katsinan ta kwana daya sannan ya dawo Abuja

A gobe juma’a ne ake kyautata zaton karbar bakuncin shugaban kasa Muhammadu Buhari a jihar Katsina domin yin jaje ga iyalan da suka fuskanci iftila’in tsawa da mamakon ruwan sama a jihar.

Da duminsa: Shugaban kasa Buhari zai ziyarci Katsina gobe

Da duminsa: Shugaban kasa Buhari zai ziyarci Katsina gobe

Gwamnan jihar Aminu Bello Masari ne ya bayyana haka a yau Alhamis a wani jawabi da aka bawa manema labarai a madadin babban mataimakin gwamnan kan yada labarai Labaran Malumfashi.

KU KARANTA: Yanzu – yanzu: Sama ko kasa, an nemi alkalin da zai shari’ar El-Zakzaky an rasa

Gwamnan ya bayyana duk da cewa shugaban kasa Buharin ya mika sakon jajen amma ya kuma nuna muradinsa na zuwa da kansa har wuraren da abin ya faru domin isar da sakon ta’aziyya da kuma jajen ga wadanda bala’in ya shafa.

“A don haka ne gwamnan ya bukaci jama’ar jihar da suyi fitar farin dango domin tarbar shugaban kasar kamar yadda suka saba cikin lumana da kwanciyar hankali”.

jawabin ya kuma bayyana cewa tsananin ruwan da akai mai hade da tsawa tare da iska mai karfin gaske ne yayi sanadiyyar yin barna sosai ga wasu unguwannin da har ta kai wasu sun rasa rayukansu, wasu kuma suka ji rauni yayin da wasu kuma gidajensu suka rushe.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel