Dalilin mu na kara kasafin kudin 2018 – Majalisar tarayya sun kare kansu

Dalilin mu na kara kasafin kudin 2018 – Majalisar tarayya sun kare kansu

‘Yan majalisar dokokin kasar sun kare kansu inda suka bayyana dalilin su na yi wa kasafin majalisa karin kudi daga naira biliyan 125 zuwa naira biliyan 139.5.

A cewarsu sun kasafin su ya yi kadan sosai, idan aka yi duba da na shekarun da suka gabata.

Sai dai kuma sun kasa bayar da wata gamsasshiyar hujjarsu na yin wawakeken karin makudan kudaden da suka yi.

Buhari ya zarge su da yin mugun kari kudade a kasafin su, kuma sun bi kasafin dalla-dalla su na zaftare kudaden, har ta kai ga ya ce da wuya ma wasu muhimman ayyukan da aka yi kudirin aiwatarwa su tabbata.

Kakakin Majalisar Tarayya, Abdulrazak Namdas, ya fitar da sanarwar cewa kasafin Majalisar Tarayya ko kusa bai kai na naira bilyan 150 da ake musu ba kafin shekarar 2015.

“Kafin 2015, ana ware wa Majalisa kasafin naira biliyan 150 a tsawon shekaru da dama. Amma a 2015 sai aka yanke shi ya koma naira biliyan 120. Cikin 2016 kuma sai aka kara zabtare shi ya koma naira biyan 115.

“Kasafin mu na 2017, naira biliyan 125 ne. Yanzu kuma na 2018, naira bilyan 139.5 ne. To kun ga har yanzu bai ma kai na naira biliyan 150 da ake yi masa kafin 2015 ba kenan.”

Daga nan majalisa ta ce ta na goyon bayan Buhari da a ja zaren aiki da kasafin kudi daga Janairu zuwa Disamba.

Dalilin mu na kara kasafin kudin 2018 – Majalisar tarayya sun kare kansu

Dalilin mu na kara kasafin kudin 2018 – Majalisar tarayya sun kare kansu

A kan haka, sun bayyana cewa a rika kai musu kasafi tun daga cikin watan Satumba su fara dubawa da wuri.

Namdas ya ce ya kamata jama’a su kula da cewa su fa jama’a suke wakilta, don haka sun saka ayyukan da za su amfani al’ummar da suke wakilta ne kai tsaye.

KU KARANTA KUMA: 2019: Manyan jam’iyyun siyasa 2 sun hade don su kwace mulki daga APC

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaba Muhammadu Buhari a jiya yayin da yake sa hannu a kan kasafin kudin shekarar 2018 a fadar gwamnatin sa a bayyana cewa 'yan majalisar tarayya sun yi masa jagwalgwalo akan kasafin kudin da sunan dubawa.

Shugaban kasar dai ya bayyana cewa 'yan majalisar sun rage kudaden ayyukan sa da suka kai akalla sama da Naira biliyan 300 akan ayyuka sama da dubu 4 da ya kuduri aniyar yi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel