Da dumin sa: Jami’an tsaron DSS sun cafke manyan kwamandojin kungiyar ISIS 2 a Abuja

Da dumin sa: Jami’an tsaron DSS sun cafke manyan kwamandojin kungiyar ISIS 2 a Abuja

Hukumar jami’an tsaro ta farin kaya (DSS) ta bayyan cewar tayi nasarar cafke wasu kwamandojin kungiyar ‘yan ta’adda ta “Islamis State of Iraq and Syria” da aka fi sani da ISIS a kauyen Kukuntu dake Gwagwalada a Abuja.

Hukumar DSS ta bayyana sunayen kwamandojin da ta kama; Rufai Sajo da Bashiru Adams.

A ‘yan kwanakin nan ne rahotannin suka bayyana cewar kungiyar ISIS tayi barazanar kawo hari Najeriya. Lamarin da ya saka hukumomi tsaurara matakan tsaro musamman a filayen tashi da saukar jiragen kasa dake fadin kasar nan.

Da dumin sa: Jami’an tsaron DSS sun cafke manyan kwamandojin kungiyar ISIS 2 a Abuja

'Yan kungiyar ISIS

A sanarwar da hukumar DSS ta fitar a yau, Alhamis, ta bakin jami’in ta, Tony Opuiyo, ta bayyana cewar ta kama kwamandojin ne tun ranar 5 ga watan Mayu bayan wani bincike da ya kai su ga gano ‘yan ta’addar.

Opuiyo ya bayyana cewar, sun kara yin nasarar cafke wani dan ta’adda, Umar Dogo, mai alaka da reshen kungiyar ta ISIS a yammacin Afrika (ISWA) a kasuwar Muda Lawal dake jihar Bauchi.

DUBA WANNAN: Da dumin sa: Dakarun soji sun yi nasarar gungun wasu ‘yan ta’adda a jihar Benuwe

Ya kara da cewa sun kama ‘yan ta’addar a daidai lokacin da suke shirye-shiryen kai wasu munanan hare-hare tare da hadin gwuiwar kungiyar Boko Haram.

Opuiyo ya sanar da cewar, hukumar DSS tayi nasarar cafke wasu kwamandojin kungiyar Boko Harma, Mohammed Saleh da aka fi sani da Azrak da kuma Iliyasu Abubakar da aka fi sani da Ruwa. An kama su ne ranakun 12 da 19 ga watan Afrilu a garin Gassol da Ardo na jihar Taraba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel