Ba’a taba samun gurbatacciyar majalisa irin na wannan lokaci ba - MURIC tayi martini ga canjin da aka samu a kasafin kudin 2018

Ba’a taba samun gurbatacciyar majalisa irin na wannan lokaci ba - MURIC tayi martini ga canjin da aka samu a kasafin kudin 2018

Kungiyar kare hakkin Musulmi MURIC ta caccaki majalisar dokoki akan zabtare kasafin kudin 2018 da yan majalisun suka yi.

A ranar Laraba, 20 ga watan Yuni ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu akan kasafin kudin na 2018, inda yayi korafi akan yanke kasafin da majalisar dokokin tayi.

Shugaban kasar yace yayinda yan majalisan suka kara kasafin su da naira biliyan 14.5, sun kuma kara ayyuka sama da 6,000 a ciki.

A wata sanarwa da aka fitar a ranar Alhamis, kungiyar Musulman sun bayyana ayyukan yan majalisan a matsayin da gangan a yunkurinsu na lalata kokarin gwamnati wajen kara kaimi akan ayyukan cigaba da take kokarin yi.

Ba’a taba samun gurbatacciyar majalisa irin na wannan lokaci ba - MURIC tayi martini ga canjin da aka samu a kasafin kudin 2018

Ba’a taba samun gurbatacciyar majalisa irin na wannan lokaci ba - MURIC tayi martini ga canjin da aka samu a kasafin kudin 2018

Kungiyar ta kuma bayyana yan majalisan a matsayin makiyan mutane inda tace ba’a taba gurbatacciyar majalisa kamar na wannan lokaci ba.

KU KARANTA KUMA: 2019: Manyan jam’iyyun siyasa 2 sun hade don su kwace mulki daga APC

Ta kuma bayyana cewa ya zama dole a dunga taya yan majalisa da yan siyasa dake kokarin kawo ci gaba da addu’o’i.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel