An ceto fiye da Mutane Miliyan 1 daga hannun 'Yan Boko Haram cikin watanni Shida - Hukumar Soji

An ceto fiye da Mutane Miliyan 1 daga hannun 'Yan Boko Haram cikin watanni Shida - Hukumar Soji

Mun samu rahoton cewa hukumar sojin kasa ta Najeriya a ranar Alhamis din da ta gabata ta bayyana cewa, ta fatattaki sahun karshen na 'yan kungiyar ta'adda ta Boko Haram zuwa cikin tafkin Chadi dake gabar iyaka da kasar Najeriya.

A yayin ganawa da manema labarai a birnin Maiduguri, kwamandan Operation Lafiya Dole, Manjo Janar Rogers Nicholas ya bayyana cewa, a yayin fatattakar 'yan ta'adda daga iyakokin kasar nan ta Najeriya sun samu nasarar ceto fiye da mutane miliyan guda cikin watannin shida da 'yan ta'adda ke garkuwa da su.

Yake cewa, sun samu babbar nasara sakamakon gudanarwar da suke aiwatarwa mai lakabin “Operation Last Hold” a yankin Arewacin Jihar Borno da a halin yanzu sun fatattaki 'yan ta'adda na Boko Haram zuwa tafkin Chadi.

Nicholas ya ci gaba da cewa, sun tsarkake duk wani lungu da sako daga 'yan ta'adda yayin da suka fattake su daga maboya da kogunan su a yankunan Arewa maso Gabashin kasar nan.

An ceto fiye da Mutane Miliyan 1 daga hannun 'Yan Boko Haram cikin watanni Shida - Hukumar Soji

An ceto fiye da Mutane Miliyan 1 daga hannun 'Yan Boko Haram cikin watanni Shida - Hukumar Soji

Kamar yadda kwamandan ya bayyana a halin yanzu mafi akasarin alkaryoyin dake yankunan Arewa maso Gabashin sun tsarkaka daga 'yan ta'adda na Boko Haram.

KARANTA KUMA: Kada Gwamnatin Tarayya ta gina Yankunan Kiwon Shanu da Kudin Al'umma

Bugu da kari hukumar ta samu nasarar kashe wasu tare cafke 'yan kunar bakin wake da dama a jihohin Borno, Yobe da kuma Adamawa cikin watanni shida da suka gabata.

Legit.ng ta fahimci cewa, akwai tukwicin Naira Miliyan 5 da hukumar sojin ta tanada ga duk wanda ya bayar da rahoton duk wani yanki da ake sarrafa bam-bamai cikin yankunan Arewa maso Gabashin Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel