Mambobin sabuwar PDP za su halarci taron APC na kasa - Baraje

Mambobin sabuwar PDP za su halarci taron APC na kasa - Baraje

Sabanin jita-jita da ake ta yayatawa mambobin sabuwar PDP karkashin jagorancin Abubakar Kawo Baraje sunce za su halarci taron jam’iyyar APC wanda za’a gudanar a ranar Asabar a Abuja.

Shugaban kungiyar, Alhaji Abubakar Baraje ya bayyana hakan a jiya Laraba, 20 ga watan Yuni a wata sanarwa daga ofishin labaransa dake Ilorin, jihar Kwara.

Baraje, wanda ya ke ta jagorantar sauran mambobin sabuwar PDP a tattaunawarsu da shugabannin APC, ya dawo daga kasar Saudiyya inda ya je yin aikin Umrah a ranar Laraba.

Ya karkata kan cewa kungiyarsa bata da wani dalili da zai hana su halartan taron.

Mambobin sabuwar PDP za su halarci taron APC na kasa - Baraje

Mambobin sabuwar PDP za su halarci taron APC na kasa - Baraje

A cewar sa, a matsayinsa na mamba a kwamitin taron jam’iyyar, ya taba halartan ganawarsu sau guda a baya, bai samu damar halartan na baya-bayan nan ba.

KU KARANTA KUMA: 2019: Manyan jam’iyyun siyasa 2 sun hade don su kwace mulki daga APC

Ya kuma ce shi ba shi da masaniya kan jita-jita dake yawo na cewar zasu fice daga jam’iyyar a ranar taron.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel