Zaben 2019: Musulmai da Kiristoci sun dukufa wajen hada hannu don kawo karshen tarzoma

Zaben 2019: Musulmai da Kiristoci sun dukufa wajen hada hannu don kawo karshen tarzoma

- Mabiya addinin kiristanci da Musulmai zasu haɗa hannu wajen samar da zaman lafiya a zaɓen 2019

- Hakan na fitowa ne daga uwar kungiyar Kiristoci matasa ta kasa

A cigaba da ƙaratowar babban zaben shekara ta 2019 kungiyar matasan kiristoci ta kasa ta bukaci kiristoci tare da musulmai da su hada kai wajen ganin sun jawo hankalin matasa domin gujewa tashin hankula a lokutan gudanar da zaben.

Zaben 2019: Musulmai da Kiristoci sun dukufa wajen hada hannu don kawo karshen tarzoma

Zaben 2019: Musulmai da Kiristoci sun dukufa wajen hada hannu don kawo karshen tarzoma

Kungiyar karkashin jagorancin Oluchukwu Nnabugwu, ta bayyanawa Jaridar vanguard hakan ne a yayin wani taro da ta gudanar mai taken "Gudunmawar matasa wajen samar da zaman lafiya mai dorewa", a garin Owerri dake jihar Imo.

KU KARANTA: Sama da jam’iyyu 100 ne zasu tsaida ‘yan takara - INEC

Nnabugwu ya ce "Kungiyar tamu yanzu haka tana kokarin shirya wani taro wanda zata ke jan hankalin matasa game da muhimmanci zaman lafiya, musamman idan aka yi duba da irin halin da kasar nan ta tsince kanta a sanadin rashin zaman lafiya, zamu yi haka ne dan cigaban kasar nan da kuma hada kan al'umma baki daya".

"A taron da zamu yi zamu gayyaci matasa da ke da zimmar samar da zaman lafiya, sannan zamu kawo rubutaccen tsari wanda za a yi amfani da shi don ganin a cimma nasarar, har wa yau, zamu samar da matasa a matsayin jami'an samar da zaman lafiya a yayin zabe mai zuwa".

Ya cigaba da cewa "Muna sa ran samun hadin-kai tare da Gudunmawa daga sarkin musulmi Alhaji Abubakar Sa'ad tare da takwaransa mai shugabantar kungiyar kiristoci ta kasa Dakta Cardinal John Onaiyekan (CAN) da sauran mayan mabiya addinin kirirstanci. Sannan muna sa ran halartar mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbanjo".

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel