Sama da jam’iyyu 100 ne zasu tsaida ‘yan takara - INEC

Sama da jam’iyyu 100 ne zasu tsaida ‘yan takara - INEC

- A cigaba da kusantowar zaben 2019, INEC ta bayyana damuwarta kan yawaitar jam'iyyu barkatai

- Amma sai dai ta ce hannunta a daure yake kasancewar ba wata doka da ta hana yin rijista ga kungiyoyin siyasar mutukar sun cika ka'ida, amma kuma ita hakan zai jawo karin kashe kudi gare ta

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana cewa jam’iyyu sama da 100 ne zasu bayyana a takardar kada kuri’ar zabe mai zuwa na shekarar 2019.

Sama da jam’iyyu 100 ne zasu tsaida ‘yan takara - INEC

Sama da jam’iyyu 100 ne zasu tsaida ‘yan takara - INEC

Shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan a yau a Abuja yayin taron masu ruwa da tsaki wajen shirya zabuka.

Zaben 2019: Sama da jam’iyyu 100 ne zasu tsaida ‘yan takara - INEC

Zaben 2019: Sama da jam’iyyu 100 ne zasu tsaida ‘yan takara - INEC

Taron da kungiyar Transition Monitoring Group (TMG), da kungiyar bayar da tallafin ta kasar Birtaniya DFID da kugiyar agaji ta Kirista ta kasa karkashin inuwar hadakar muryar al’umma (V2P) ne suka shiriya.

Mahmood Yakubu ya tabbtar da cewa kungiyoyin siyasu 138 ne suke neman sahale musu don su zama cikakkiyar jam’iyyar siyasa

KU KARANTA: An damke ƴan ƙasashen ƙetare 300 a wurin rijistar katin zabe

Amma sai dai shugaban INEC din ya bayyana damuwarsa kasancewar hukumar bata ikon hana kungiyoyin lasisin zama jam’iyya mutukar sun cika sharruda, wanda yawaitarsu jam’iyyun na iya sanya hukumar kashe kudade masu yawan gaske wajen shirya zabe.

Sannan ya kuma kara da cewa jami’an kula da shige da fice ta kasa (NIS) sun samu nasarar cafke bakin haure har 300 yayin da suke yunkurin rijistar katin zaben.

“Daga ranar 24 na watan Mayu da hukumar tayi lissafi, ta yiwa nasarar sake yiwa karin mutane miliyan tara rijistar wanda hakan ya kai yawan mutanen da su kayi rijista zuwa miliyan 80m”

INEC din kuma ta yi hadin gwuiwa da sauran hukumomin tsaro domin fito da sabbin hanyoyin magance biyan kudi don a kadawa jam’iyyu kuri’a. a cewar Farfesa Yakubu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel