Bai kamata ka sanya hannu kan Kasafin Kudin 2018 ba - 'Yan Najeriya ga Shugaba Buhari

Bai kamata ka sanya hannu kan Kasafin Kudin 2018 ba - 'Yan Najeriya ga Shugaba Buhari

Ko shakka babu da misalin karfe 12.05 na ranar Larabar da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan kasafin kudin 2018 a fadar gwamnatin sa ta Villa dake babban birnin kasar nan na Abuja.

Sai dai shugaba Buhari yayin rattaba hannu ya yi baƙin cikin dangane da yadda Majalisar Dokoki ta tarayya ta aiwatar da wasu sauye-sauye cikin kasafin kudin sabanin yadda ya gabatar a gaban ta tun a watan Nuwamba na shekarar 2017 da ta gabata.

A sanadiyar haka ne shugaba Buhari ya bayyana cewa, akwai yiwuwar rashin aiwatar gami da dabbaka wannan kasafin kudin wajen gudanar da al'amurran kasar nan sakamakon sauyen-sauyen da majalisar ta gudanar.

Shugaba Buhari ya zargi wasu 'yan Majalisar na tarayya da yin ƙari cikin kasafin kudin majalisar su ta Dokoki na tarayya daga Naira Biliyan 125 zuwa Naira Biliyan 139.5.

Shugaba Buhari yayin sanya hannu kan Kasafin Kudin 2018

Shugaba Buhari yayin sanya hannu kan Kasafin Kudin 2018

Hakazalika shugaba Buhari ya zargi Majalisar da ƙara adadin ayyuka na su na karan kansu cikin kasafin kudin zuwa Naira Biliyan 578 sabanin ayyukan da ya gabatar na kimanin Naira Biliyan 347.

KARANTA KUMA: Zaben 2019: Har yanzu ba mu amince da Shugaba Buhari ko wani 'Dan Takara ba

A yayin mayar da martani dangane da wannan zargi, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Bala Ibn Na’Allah da kuma shugaba na Majalisar Wakilai, Alhassan Ado-Doguwa sun bayyana cewa, muddin suka zuba idanu kan kasafin kudin da shugaba Buhari ya gabatar ba tare da aiwatar da sauye-sauye ba to kuwa za su shiga cikin rudani da al'ummar da suka kada ma su kuri'u na kujerun da suke kai a yanzu.

Legit.ng ta kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito ta fahimci cewa, a yayin haka ne wasu 'yan Najeriya suka bayyana cewa ko kadan bai kamata shugaba Buhari ya sanya hannu kan kasafin kudin ba sakamakon ikirarin sa na sauye-sauye da majalisar Dokokin tarayya ta aiwatar.

Da yawan 'yan Najeriya sun bayyana ra'ayoyin su a shafukan su na sada zumunta inda suka da sakonnin su ka tsaye zuwa ga shafin shugaba Buhari a shafin sa na twitter kamar haka:

A yayin haka kuma jaridar Legit.ng a ranar Larabar da ta gabata ta ruwaito cewa, shugaba Buhari ya bayyana dalilin sa na rattaba hannu kan kasafin kudin 2018 da cewar ya gudun kawo tsaiko cikin tattalin arzikin kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel