Karshen lalacewa: Wani uba ya yiwa diyar sa mai shekara 1 kacal fyade

Karshen lalacewa: Wani uba ya yiwa diyar sa mai shekara 1 kacal fyade

Wata kotun majistare dake zaman ta a Ikeja ta jihar Legas tayi umarnin a tsare wani magidanci mai shekaru 36 a gidan yari na Kirikir bisa zargin sad a aikata laifin fyade ga diyar cikin sa mai shekara daya kacal a duniya.

Lalataccen mahaifin, Olaitan Adewoye, zai kasance a gidan yari na Kirikiri na tsawon kwanaki 21 kafin darektan sashen kula da kararraki na jihar Legas ya bayar da shawarar matakin day a kamata a dauka a kan mutumin bayan y agama nazarin takardun tuhumar da ake yi masa.

Dan sanda mai gabatar da kara, Christopher John, ya shaidawa kotun cewar, Adewoye, mazaunin gida mai lamba 10 dake kan titin Arogundade dake rukunin gidajen Harmony a unguwar Ajah a garin Legas, ya aikata laifin ne ranar 17 ga watan Mayu.

Karshen lalacewa: Wani uba ya yiwa diyar sa mai shekara 1 kacal fyade

Gudumar kotu

Dan sanda John ya sanar da kotun cewar, Adewoye ya yiwa diyar ta sa fyade ne bayan mahaifiyar shi da yarinyar a gida tare da shaidawa kotun cewar mahifiyar yarinyar ta gano hakan ta faru ne bayan ta kai yarinyar asibiti domin a duba abinda ke damun ta saboda yawan kuka da take yi da an motsa ta.

DUBA WANNAN: Yadda wani ango ya yiwa amaryar sa kisan gilla wata 4 kacal bayan daura masu aure

John ya kara da cewa, mahaifiyar yarinya bat a bar yarinyar da kowa ba sai mahaifin nata.

An kama mahaifin yarinyar ne bayan mahaifiyar yarinyar ta shigar da korafi ofishin ‘yan sanda.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar, laifin da Adewoye ya aikata na da hukuncin daurin rai-da-rai a gidan yari.

An daga sauraron karar zuwa ranar 11 ga watan Yuli.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel