Ya cinnawa gidan makwabcin sa wuta saboda ya fin a shi kyau, an gurfanar das hi gaban kotu

Ya cinnawa gidan makwabcin sa wuta saboda ya fin a shi kyau, an gurfanar das hi gaban kotu

A yau, Alhamis, hukumar ‘yan sanda ta gurfanar da wani mutum, Oshajare Ohutimi, mai shekaru 37 a gaban wata mai daraja ta 1 dake Kubwa a Abuja bisa zargin sad a cinnawa gidan makwabcin sa wuta.

Ana tuhumar Ohutimi da laifin aikata mugunta da gan-gan, zargin da ya ki yarda ya amsa a gaban kotun.

Dan sanda mai gabatar da kara, Babajide Olanipekun, ya shaidawa kotun cewar mutumin da aka cinnawa gidan sa wutar ne mai suna Peter Ezemba ya shigar da korafin ofishin ‘yan sanda na Kubwa ranar 17 ga watan Yuni.

Ya cinnawa gidan makwabcin sa wuta saboda ya fin a shi kyau, an gurfanar das hi gaban kotu

Gobara

Dan sanda Olanipekun ya shaidawa kotun cewar, Ohutimi, ya aikata laifin ne lokacin da Ezemba ba ya gida kuma ya cinna wutar ne ta cikin silin din gidan makwabcin na sa.

Dan sandan ya kara da cewa Ohutimi ya saka wutar ne dag an-gan domin kawai ya jawowa makwabcin sa asara saboda kyashi tare da rokon kotun da kada ta bayar da belin sa saboda zai iya kara aikata laifin cinna gobara a gidan makwabcin na sa.

DUBA WANNAN: Da dumin sa: Buhari ya zubar da hawaye yayin da ya ziyarci kasuwar Azare da gobara ta lalata,kalli hotuna

Saidai lauya Moses Ugwummadu, dake kare wanda ake tuhuma, ya roki kotun da tayi watsi da maganganun dan sanda Olanipekun tare da neman belin wanda yake karewa.

Alkalin kotun, Abdulwahab Mohammed, ya amince da bukatar bayar da belin Ohutimi bisa sharadin zai ajiye N300,000 a kotun da kuma wanda zai tsaya masa, wanda tilas ya kasance sananne a unguwar da yake zaune a Abuja.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel