2019: Manyan jam’iyyun siyasa 2 sun hade don su kwace mulki daga APC

2019: Manyan jam’iyyun siyasa 2 sun hade don su kwace mulki daga APC

Manyan jam’iyyun siyasa biyu sun hade a shirye-shiryen da akeyi na siyasar 2019 mai zuwa.

A ranar Laraba, 20 ga watan Yuni, Jam’iyyar Nigeria Intervention Movement ta hade da jam’iyyar Alliance for New Nigeria.

A cewar wata sanarwa daga shugabannin NIM, Olisa Agbakoba da Abduljalil Tafawa-Balewa sun ce kungiyar ta yanke wannan shawara ne a Lagas a ranar Laraba.

Shugabannin kungiyar sunce yan Najeriya da dama sun ji dadin yadda siyasar Najeriya ke tafiya.

Sunce son zuciyar shugabannin siyasa na cigaba da kawo cikas a shugabancin Najeriya.

Sunce don haka sun billo da wannan sabuwar hanya domin ceto kasar daga halin da take ciki.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa shugabannin kungiyar matasan Kudu sun amince da shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sake takara.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Hukumar DSS ta kama tsohon gwamnan jihar Benue, Suswam

A wajen wani taro a Lagas, shugabannin matasan sun kuma nuna ammincewarsu da shugaban hafsan sojin Najeriya, Janar Tukur Yusuf Buratai da sauran shugabannin tsaro.

Kungiyar ta bayyana irin tarin nasarorin da gwamnatin shugaba Buhari ta samu a fannin tattalin arziki, tsaro da kuma yaki da cin hanci da rashawa a matsayin dalilin tsayar da shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel