Dalilin da yasa aka taso 'Keyar 'yan Najeriya 34 daga Kasar Amurka

Dalilin da yasa aka taso 'Keyar 'yan Najeriya 34 daga Kasar Amurka

A ranar Larabar da ta gabata ne Kasar Amurka ta taso keyar wasu 'yan Najeriya 34 zuwa kasar su sakamakon wasu miyagun laifuka da suka aikata da ya sabawa dokoki na ci gaba da zaman su a Kasar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, wannan mutane sun sauka da misalin karfe 2.30 na yammacin ranar Larabar da ta gabata a filin jirgin sama na Murtala Muhammad dake jihar Legas.

Legit.ng ta fahimci cewa, wannan mutane 34 sun hadar da maza 32 da kuma mata 2 da wani jirgi na kamfanin Omni Air International mai lambar W342AX ya yo jigilar su zuwa Najeriya.

Dalilin da yasa aka taso 'Keyar 'yan Najeriya 34 daga Kasar Amurka

Dalilin da yasa aka taso 'Keyar 'yan Najeriya 34 daga Kasar Amurka

Wata majiyar rahoto daga hukumar hijira ta Najeriya ta bayyana cewa, Kasar Amurka ta yi wannan kora ta musamman ne ga wannan mutane sakamakon laifukan da suka aikata da suka hadar da; zamba, cin zarafi, kisan kai, mallakar haramtattun ababe da makamantan laifuka.

KARANTA KUMA: Zaben 2019: Atiku shine zabin da zai sanya Najeriya ta fuskanci Alƙiblar ta - Ben Bruce

Kakakin hukumar 'yan sanda na reshen filin jirgin saman, DSP Joseph Alabi, shine ya bayar da tabbacin wannan rahoto kamar yadda shafin jaridar The Punch ya bayyana.

DSP Joseph ya kara da cewa, mutane 25 daga cikin su sun aikata miyagun laifuka ne inda guda daya daga cikin su yake harkokin kayen maye yayin da sauran suka aikata laifuka da suka sabawa dokar hijira ta Amurka.

A yayin haka kuma, jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, kungiyar Kirista ta Najeriya ta yi karin haske dangane da amincewa da goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin dan takara a zaben 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel