Kasafin kudin 2018: Zamu shirya taron yan jarida na musamman domin raddi ga Buhari – Majalisar dattawa

Kasafin kudin 2018: Zamu shirya taron yan jarida na musamman domin raddi ga Buhari – Majalisar dattawa

Majalisar dattawa Najeriya ta saki jawabi kan bacin ran shugaba Muhammadu Buhari ya nuna kan sauye-sauyen da yan majalisa suka yi cikin kasafin kudi 2018.

Kakakin majalisar dattawa, Sanata Sabi Abdullahi, ya sakin jawabin nuna goyon baya ga jawabin yan majalisan wakilai ta saki da niyyan martini ga shugaba Muhammadu Buhari.

A jawabin da ya saki, Sabi Abdullahi yace: “Majalisar dattawa ta ga jawabin da takwararmu, majalisar wakilai, ta saki a matsayin martini ga shugaba Muhammadu Buhari kan jawabin da yayi wajen rattaba hannu kan kasafin kudin 2018.”

A sani cewa shugabancin majalisun biyu sun umurci shugabannin kwamitocin kasafin kudi su bayar da bayani dalla-dalla kan abubuwan da shugaba kasa y ace domin amfanan al’umma.

Bayan sun shirya, za’a gabatarwa yan jarida a hira ranan Juma’a, 22 ga watan Yuni, 2018.”

KU KARANTA: An damke ƴan ƙasashen ƙetare 300 a wurin rijistar katin zabe

Kasafin kudin 2018: Zamu shirya taron yan jarida na musamman domin raddi ga Buhari – Majalisar dattawa

Kasafin kudin 2018: Zamu shirya taron yan jarida na musamman domin raddi ga Buhari – Majalisar dattawa

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa shugaba Buhari Shugaba Buhari ya nuna bacin ransa kan canja-canjen da majalisar dokokin tarayya tayi ckin kasafin kudin na rage-rage da kare-kare.

Buhari yace majalisar dokokin tarayya ta zabge kudi 347 billion Naira cikin ayyukan 4,700 da aka gabatar ma ta amma suka sanya ayyukan kansu guda 6,403 na kimann kudi 578 billion Naira.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel