Yan kunar bakin wake 2 sun mutu a kasuwar mammy dake Maiduguri

Yan kunar bakin wake 2 sun mutu a kasuwar mammy dake Maiduguri

Rundunar yan sandan jihar Borno sun ce yan kunar bakin wake mata biyu sun mutu a daren ranar Laraba yayinda suke kokarin tayar da bam a wajen shakatawar sojoji a Maiduguri.

Edet Okon, kakakin yan sandan ya bayyana hakan a wata sanarwa da suka saki a Maiduguri.

Okon ya bayyana cewa sojoji sun harbe yar kunar bakin wake ta farko yayinda take kokarin siyan tikitin shiga kasuwar Mammyn, inda sojojin ke shakatawa. Sojojin sun harbe ta bayan sun yi zargin yar kunar bakin wake ce.

Yan kunar bakin wake 2 sun mutu a kasuwar mammy dake Maiduguri

Yan kunar bakin wake 2 sun mutu a kasuwar mammy dake Maiduguri

“Bam din ya tashi sannan ya kashe yar kunar bakin wake ta farko yayinda ta farko ke kokarin tayar da nata bam din a cikin adaidaita sahu. Direban adaidaitan ya gudu ya bar wajen.

“Sakamakon tashin bam din, yan kunar bakin waken biyu suka mutu a take yayinda mutane 15 suka ji rauni sannan aka kai su asibiti cikin gaggawa.

KU KARANTA KUMA: 2019: Matasan Kudu sun amince da Buhari ya sake takara

“A halin yanzu an tattara wajen da lamarin ya faru sannan kuma abubuwa sun daidaita a wajen."

Daga karshe an bukaci mutane da sun hakalta sannan su zamo masu lura da mutane domin kai karar duk wani motsi da basu aminta da shi ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel