Yanzu-yanzu: Buhari ya isa jihar Bauchi

Yanzu-yanzu: Buhari ya isa jihar Bauchi

Shugaba Muhammadu Buhari ya isa jihar Bauchi jajintawa mutan jihar Bauchi kan iftila'in da ya faru da su.

Jirgin da ke dauke da shugaba Buhari ya dira a babban filin jirgin saman Sir Abubakar Tafawa Balewa ne misalin karfe 9:30 a yau Alhamis, 21 ga watan Yuni, 2018.

Gwamnan jihar Bauchi, Mohammed Abubakar da kakakin majalisar dokokin jihar, Kawuwa Damina, suka tarbi shugaba Buhari a filin jirgin saman.

Sauran da suka tarbeshi sune Diraktan hukumar agaji na gaggawa wato NEMA, Mr Mustapha Maihaja; sakataren gwamnatin tarayya, Mr Mohammed Nadada, da kuma wasu manyan jami'an gwamnatin jihar.

Zamu kawo muku cikakken rahoton.....

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel