Shell zata biya $3.6b ga kauyukan da aikin tatsar mai ya gurbata

Shell zata biya $3.6b ga kauyukan da aikin tatsar mai ya gurbata

- An dade ana gurbata yankunan da ake tatsar mai a Neja Delta

- Sai yanzu ne bayan shekaru 40 ake kokarin biyansu diyya

- A baya har rataye masu rajin kare hakkin yankin gwamnatin Abacha tayi

Shell zata biya $3.6b ga kauyukan da aikin tatsar mai ya gurbata

Shell zata biya $3.6b ga kauyukan da aikin tatsar mai ya gurbata

Shekaru 40 kenan ake ta gurbata yankunan Neja Delta, wanda a nan ne ake tatsar arzikin da ake sha duk adin Najeriya.

Kotun Najeriya tace Shell zai biya akalla tiriliyan daya na nairori ga wadanda suka rasa muhallansu da gonakinsu, domin ko kifi ya daina rayuwa a yankin.

Ruwan sha ma ya gurbace, balle uwa uba, noma da kiwo.

Kamfanin dai ya bada hakuri, yace zai yi duk yadda zayyi don gyara kura-kuransa.

DUBA WANNAN: Hutun sallah ya sauko da kasuwannin hannayen jari daga tiriliyan tara da doriya

A baya, lokacin mulkin soja, an sha kame da kashe wadanda ke kokarin jawo hankalin gwamnati da duniya kan yadda ake gurbata yanayin.

Neja Delta ita ta bada mai da ake titi da ayyukan ci gaba a duk fadin kasar nan, wanda ba don ita ba, da yanzu sai dai a kirga mu cikin talakawan duniya masu hayayyafa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel