Atiku ya ziyarci Jonathan, sun ba da tabbacin cewa PDP zata lashe zabe mai zuwa

Atiku ya ziyarci Jonathan, sun ba da tabbacin cewa PDP zata lashe zabe mai zuwa

A ranar Laraba, 20 ga watan Yuni, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar sun ba da tabbacin cewa jam’iyyar PDP zata dawo kujerar mulki a 2019, jaridar The Nation ta ruwaito.

Legit.ng ta tattaro cewa shugabannin biyu sun yi wannan zance ne a lokacin da Atiku ya kai wata ziyarar ban girma ga tsohon mataimakin shugaban kasar a gidan sa dake a jihar Bayelsa ranar Larabar da ta gabata.

Jonathan a wata sanarwa daga kakakinsa, Ilechukwu Eze, yace akwai alamu na cewa PDP zatayi nasara a 2019, inda yace jam’iyyar na da dukkan abubuwan da zai kai ta ga lashe zabe mai zuwa.

Atiku ya ziyarci Jonathan, ya ba da tabbacin cewa PDP zata lashe zabe mai zuwa

Atiku ya ziyarci Jonathan, ya ba da tabbacin cewa PDP zata lashe zabe mai zuwa

Jonathan yace yana jin dadin dogon alaka dake tsakaninsa da Atiku, wanda ya soma tun a lokacin da yake a matsayin mataimakin gwamnan Bayelsa.

Atiku yace lallai PDP kadai ce ke da karfin lashe zaben shugabancin kasa a 2019.

A halin da ake ciki, Atiku Abubakar ya yabawa tsohon shugaban kasar nan Goodluck Jonathan tare da fada masa cewa tarihi ba zai taba mantawa da shi ba.

KU KARANTA KUMA: 2019: Matasan Kudu sun amince da Buhari ya sake takara

Atiku wanda yanzu haka yake wani rangadi a fadin kasar nan domin neman amincewar mutane su goyi bayan sa, ya cewa Jonathan babban gwarzo ne da ya mika mulki da ya fadi zaben 2015 ba tare da wata hatsaniya ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel